manufar da'awar salafiyyah.

          KAJI TSORAN ALLAH / KADA KIYAYYA TA HANAKA FADIN GASKIYA......
'
'YAN-UWA-
Insha Allahu / Zanyi wani abu da Bahaushe yake cewa......
  1. QARSHEN TIKA-TIKA-TIK...
"
MAGANACE ZANYI AKAN 'YAN-SALAFIYYA.....
'
DAN-UWA / 'YAR-UWA-
Lallai yana da kyau Mutsaya mu Karanta Wannan Sakon......
'
BA DON KOMAI BA-
Sai don mu warware Shubuhohin da wasu Miyagun Mutane Suke ta yadawa acikin Al'Ummar musulmi. Don su raba su Da Alkairan da muka zo musu dashi.....
WANNAN KENAN....
'
KAMAR YADDA NACE-
'
1- ME AKE NUFI DA SALAF ??
'
2- SUWAYE 'YAN-SALAFIYYA ??
'
3- MENE NE MANUFAR 'YAN SALAF ??
'
Wannan Shine abin da Zanyi magana Akansa, Da izinin Allah (s.w.t).....
"
AGURGUJE / KAMAR YADDA NACE-
'
1- Me ake nufi da Salaf ???
'
AMSA-
salaf ayaren Larabci / yana Nufin abin da ya Wuce / Alkairi, ko Sharri,....
'
ASHARI'ANCE KUMA-
salaf na Nufin Magabata akan Duk wani aikin Alkairi / wato....
* Annabi (s.a.w) Da-
* Sahabbansa (r.a) Da-
* Tabi'ai, Da kuma Tabi'it-tabi'ina.,
'
WANNAN KENAN....
"
TAMBAYA TA BIYU...
2- Suwaye 'yan- Salafiyya ???
'
AMSA...
Mune 'yan-salafiyya / Kuma kalmar Salafiyya. Na Nufin masu bin Tafarkin magabata, Wanda akafi sani da ( Salafus-saleh )..
* Manzon Allah (s.a.w)-
* Sahabbansa (r.a)-
* Tabi'ai Da Tabi'it-tabi'in...
'
MU 'YAN SALAFIYYA...
Bama bin fahimtar kowa a addini/ Inba fahimtar da salaf sukayi wa Addinin ba.... MA'ANA....
Dole ne fahimtarka a addini tayi dai-dai da yadda Magabata..
(salafus-saleh) suka faimci addini..
WANNAN KENAN.....
"
TAMBAYA TA UKU-
3- Mene ne Manufarmu. Mu 'yan Salafiyya ???
"
AMSA-
DA FARKO DAI.....
Mu ba Kugiya bane, mu akaran kanmu / kuma ba'a Karkashin wata Qungiya muke ba...
'
SA'ANNAN....
Mu ba munaiwa Wasu Qungiyoyine acikin Gida, ko a waje Aiki ba.... MA'ANA....
Mu ba Members Din kowa bane acikin Qasarmu ko awajen Qasarmu ba.....
'
A'ah-
mu Muna aikine Na Da'awa/ wanda wannan Da'awar. Itace abar da muka fahimta mafi Girma a addinin Musulinci....
WANNAN KENAN....
'
NA BIYU-
Mu ba 'yan Ta'adda bane / kuma mu bamu yarda da Cin Zarafin Mutane ba....
'
SA'ANNAN-
Mu bamu yarda da Maqalewa Mazhaba Guda daya tak ba...
'
MA'ANA...
Bamu yarda da abi imam malik shi kadai ba...
'
A'ah....
* IMAM MALIK-
malamine agunmu...
'
* IMAM SHAFI'E-
Shima malamine agunmu...
'
* IMAM AHMAD BIN HAMBAL-
Shima malaminmu ne...
'
* IMAM ABU HANIFA-
Shima malamine agunmu kamar yadda Sauran suke malamai agunmu....
'
WADANNAN MALAMAN-
Gaba dayansu mun yarda dasu, kuma muna amfani da Alkairan da suke dashi....
'
AMMA...
Bamu yarda da aware wani malami daga Cikinsu amatsayin abin bi ba...
'
A'ah...
Mu agunmu Annabi (s.a.w) shi kadaine Ya Cancanta abi / Domin shine Wanda baya kuskure...
'
SA'ANNANMA WANI ABIN FARINCIKI....
Gaba daya malamannan dana Lissafo / Dukkaninsu Sunce...
Idan maganarsu taci karo data Annabi (s.a.w) / To abar maganarsu adauki ta Manzon Allah (s.a.w)...
WANNAN KENAN....
'
SA'ANNAN...
yana daga Cikin manufofinmu shine....
'
Karantar da Al'ummar musulmi..
'
Taimakon marayu...
'
Gina asibitoci na Musulinci....
'
yaki da Shirka da Bid'a....
'
Kare martabar magabata.....
'
Taimakon Gajiyayyu.....e.t.c.......
'
WANNAN SHINE MANUFARMU ATAQAICE......,
'
DAN-HAKA...
duk wanda bai sanmu ba, to ga yadda muke......
"
'YAN-UWA...
anan zan Dakata Ina mana fatan Alkairi.....
    Bissalam
  • Domin karin bayani akan manufarmu duba wannan gajeren bidion dake kasa.
  • Comments

    Post a Comment